25 Faburairu 2016 - 12:39
Kasar Ivory Coast Ta Ba Wa Blaise Compaore Shaidan Zama Dan Kasar

Kasar Ivory Coast Ta Ba Wa Blaise Compaore Shaidan Zama Dan Kasar

Gwamnatin kasar Ivory Coast ta sanar da cewa ta ba wa hambararren shugaban kasar Burkina Faso Blaise Compaore takardar zama dan kasar lamarin da zai iya yin kafar ungulu ga kokarin gwamnatin kasar Burkina Fason na mika mata shi don hukunta shi kan zargin da ake masa na hannu cikin kisan gillan da aka yi wa tsohon shugaban kasar Thomas Sankara

A wata sanarwa da gwamnatin ta fitar ta ce ta ba wa tsohon shugaba Compaore da dansa Paul Francois takardar zama dan kasar Ivory Coast, don haka yanzu sun zama cikakkun 'yan kasa.

A watan Disambar shekarar da ta gabata ce gwamnatin kasar Burkina Fason ta fitar da sammacin kamo mata tsohon shugaba Compaoren wanda ke gudun hijira a kasar Ivory Coast saboda zargin da take masa na hannun cikin kisan gillan da aka yi wa tsohon shugaban kasar Thomas Sankara shekaru 30 din da suka gabata.

A bisa dokokin kasar Ivory Coast din, gwamnati ba ta da ikon mika wani dan kasar ga wata kasa ta waje don hukunta shi. Hakan ne ma ya sanya ake ganin ba wa Compaore dan kasa din zai zamanto kafar ungulu ga kokarin mahukuntan Burkina Fason na dawo da shi gida don hukunta shi.288